Monday, 1 July 2013

AZUMI A MAHANGAR SHARIA(4)
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيم ، والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وأصحابه ومن ولاه

Azumi yana tabbata ya zama wajibi akan Musulmai da dayan abubuwa guda biyu.

1- Ganin Jinjirin wata na Ramadhadan.

2-Cikar watan Sha’aban kwana talatin(30) dai dai.

Wan nan shine Sharia ta tsayar bisa hujjoji daga  Allaah swt da  kuma Sunnar Manzon Allaah(s.a.w).

Allaah yace
فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ
“DUK WANDA YA HALARCESHI(watan Ramadhan) TO YA AZUMCESHI”

Ma’ana wanda akaga wata kuma yana raye to yayi Azumin wantan Ramadhana, bashi nufin sai kowa yaga Watan da kansa.

Manzon Allaah(s.a.w) yace:
«إِذَا رأيتُمُ الهلالَ فصوموا»
“IDAN KUKAGA JINJIRIN WATA,TO KU AZUMCESHI”

Hanyoyin da ake tabbatar da ganin wata daga Bakin Manzon Allaah(s.a.w).

A-Idan anga jinjirin wata domin Manzon Allaah(s.a.w) yace:
فقالَ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا رَأيتُمُ الهلالَ فصُوموا وإِذَا رَأَيْتُمُوه فأفْطِروا»، متفق عليه
“IDAN KUNGA JINJIRIN WATA TO KU AZUMCESHI,HAKA KUMA IDAN KUNGANSHI TO KU CI(lokacin Sallah)”.

Haka kuma yazo daga gareshi dai yace:
قال صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إن شَهِدَ شاهدان مُسْلمانِ فصومُوا وأفْطُروا»، رواه أحمد  .[إسناده لا بأس به على اختلاف فيه وله شاهد عند أبي داود والدارقطني وقال: هذا إسناده متصل صحيح].
“IDAN MUSULMAI GUDA BIYU SUKA SHAIDA SUNGA WATA,TO KUYI AZUMI,KUMA KUCI(idan watan Shawwal ne)”.
[Sai dai wan nan ruwayar bata da laifi a bisa sabani, kuma a wajen Abu Daud da Daruqud'niy akwai Shahid,har ya kara da cewa isnadinsa ya sadu kuma Saheehi ne].

B-Cikar watan Sha’aban kwana 30 koda ba’aga watan ba indai yakai kwana talatin to Azumi ya kama,saboda fadin Manzon Allaah(s.a.w):
«صُوموا لِرؤيتِهِ وأفْطروا لرؤيته فإن غُمِّي عليكُمْ الشهر فعدوا ثلاثين»، رواهُ مسلم.
‘KUYI AZUMI SABODA GANIN WATA,KUMA KUCI SABODA GANINSA,AMMA IDAN AKA BOYE MUKU WATAN,TO KU KIRGA KWANA TALATIN”.

Wan nan yana nuna cewa wata yakan zamo kwana ishirin da tara(29) mafi yawa,ko kuma Talatin(30) idan ba’a ganshi ba.

Sau da yawa Watanni a jere sukan yi kwanaki 29,kamar wata 2,3 ko 4.
Haka kuma sukanyi kwanaki 30 a jere shima kamar yanda muka fada a sama.
Wata hikima ta Manzon Allaah(s.a.w), sai yace”Idan aka boye muku shi, to sai ku kidaya masa 30,ashe asalinsa 29 ne,saifa idan ba’a ganshi ba,kodai anyi girgije ko kuma dai wani dalili,to sai a kirga 30.

Domin fito da hukuncin fili, sai Aishah(r.a) tace:
«كانَ النبيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَتحفَّظُ من شعبانَ ما لا يَتَحَفَّظ من غيرهِ ثم يصوم لرؤيةِ رمضان فإنْ غُمَّ عليه عَدَّ ثلاثين يوماً ثم صام»، وأخرجه أيضاً أبو دَاود والدَّارقطنيُّ وصحَّحهُ.
“MANZON ALLAAH(S.A.W) YA ZAMA YANA KIYAYE WATAN SHA’ABAN FIYE DA KO WANE WATA,SAN NAN KUMA SAI YAYI AZUMI IDAN ANGA RAMADHANA. 
AMMA IDAN AKA BOYE MISHI WATAN,SAI YA KIRGA KWANA TALATIN,SAN NAN YA DAUKI AZUMI”.

Wan nan yana kara fito da Mas’alar ganin wata fili,cewa kodai kwana 29 ne da ganin wata,ko kuma 30 koda watan ya buya.
Hadeethin da Manzon Allaah(s.a.w) yayiwa Matansa Yaji tsawon Wata guda ya kuma fito da batun fili.

Domin bayan kwana 29 daya shigo gida,sai Matarsa dayafi so tace,bakace wata guda ba ne?  Gashi kuma yau kwana 29.
Sai yace ai Wata kwana 29 ne.

Ruwayar Abdullahi ibn Umar(r.a) ta kara fito da batun a sarari kamar haka:
عن نافع عن ابن عمر - رضي الله عنهما - قال : قال رسول الله - صلى الله عليه وسلم - : "إِنَّمَا الشَّهْرُ تِسْعٌ وَعِشْرُونَ فَلاَ تَصُومُوا حَتَّى تَرَوْهُ، وَلاَ تُفْطِرُوا حَتَّى تَرَوْهُ، فَإِنْ غُمَّ عَلَيْكُمْ فَاقْدِرُوا لَهُ"] أخرجه أبو داود في سننه في كتاب الصيام / باب الشهر يكون تسعاً وعشرين (2321) ، وأحمد في مسنده (4483) ، قال الألباني عن حديث ابن عمر - رضي الله عنهما - : صحيح دون قوله (فكان ابن عمر) [صحيح سنن أبي داود للإمام الألباني (2\49) رقم الحديث (2320)]
“Manzon Allaah(s.a.w) yace:
‘'WATA KWANA ASHIRIN DA TARANE(29), KADA KUYI AZUMI HAR SAI KUN GANSHI,KADA KUMA KUCI HAR SAI KUN GANSHI.
AMMA IDAN YA BUYA GAREKU, TO KU KIRGA MISHI”.

Haka ya kuma zuwa cikin fadin Manzon Allaah(s.a.w) yace:
“عن النبيِّ - صلى الله عليه وسلم - أنهُ قال: "إنّا أُمَّةٌ أُمِّيةٌ لا نَكتُبُ ولا نَحسُبُ ، الشهرُ هكذا وهكذا. يَعني مرَّةً تسعةً وعشرينَ ومرَّةً ثلاثين".
“LALLAI MU MUTANE NE UMMIYYAI, BAMA RUBUTU KUMA BAMA(rubuta) LISSAFI, WATA DAI HAKA NE DA KUMA HAKA(na farko ya lankwashe yatsansa daya,bayan ya kirga yatsunsa su uku)”.
Yana nufin wani lokaci 29,wani kuma lokaci 30.

Idan Musulmi yasan wa’yan nan maganganu daga bakin fiyayyen Halitta,ina batun Gardama idan wata yayi kwana 29 ko kuma 30?
Allaah ya shiryar damu!!!

Maganganun Malaman Mazhabobi akan ganin Wata,da kuma suwaye idan sunga wata ake yarda dasu.
Su waye ya kamata su sanar da anga wata???.

Idan anga Wata amma Shugaba bai yarda da masu ganin ba menene hukuncin ganin Watan nasu,kuma me yakamata suyi???

نسأل الله تعالى أن يجعلنا وإياكم من عتقاء النار وأن يرحمنا ويغفر لنا وان يعيد علينا رمضان مرات عديدة وكرات مديدة.
وآخر دعوانا أن الحمد لله رب العالمين

No comments:

Post a Comment