Monday, 1 July 2013

AZUMI A MAHANGAR SHARIA(5)

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيم ، والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وأصحابه ومن ولاه

Suwaye idan sunga Wata ake karba,kuma yaya ake karbar???
Waye yake bada Sanarwa idan ance anga Wata???
Kuma sai mutane nawane idan sunga Wata ya zama hujjah akan musulmai su tashi da Azumi???

Wa’yan nan tambayoyi zasu fito mana da yanda sunnah ta koyar da ganin wata,domin abin yafi Farin Wata dan daren goma shadu(14) haske da kuma fitowa fili.

MASU GANIN WATA AYI AIKI DASHI A MUSULUNCI:

1-Yana kasantuwa da ganin Mutum Daya,amma kuma yazama Musulmi, saboda hadeethin Ibn Umar(r.a) dayazo ya gayawa Manzon Allaah(s.a.w) yaga Wata,sai ya dauki Azumi kuma yayi Umarni da Mutane su dauka’ haka kuma lokacinda wani Balaraben Kauye yace yaga wata.

Manzon Allah(s.a.w) tambayarsa yayi idan shi musulmi ne,dayce ‘E’ sai ya bada Umarni da ayi shela Mutane su dauki Azumi,ga yanda hadeethin yazo kamr haka:
A-عن ابن عمر - رضي الله عنهما - قال : "تَرَاءى النَّاسُ الهِلاَلَ فَأَخْبَرْتُ رَسُولَ الله - صلى الله  عليه وسلم - أنِّي رَأَيْتُهُ فَصَامَ وَأَمَرَ النَّاسَ بِصِيَامِهِ" ]أخرجه أبو داود في سننه في كتاب الصيام / باب في شهادة الواحد على رؤية هلال رمضان (2343) ، قال الألباني : صحيح [صحيح سنن أبي داود للإمام الألباني (2\55) رقم الحديث (2342)] ، وقال ابن حجر : صححه ابن حزم [تلخيص الحبير لابن حجر (2\187) رقم الحديث (879)]
Daga Ibn Umar(r.a) yace:”MUTANE SUNGA JINJIRIN WATA,SAI NA BAWA MANZON ALLAAH(S.A.W) CEWA NIMA NAGANSHI,SAI YAYI AZUMI,KUMA YA UMARCI MUTANE SUMA SU TASHI DA AZUMI”.
S
ai kuma Hadeethin kuma Hadeethin Ibn Abbas(r.a) kamar haka:

B-عن ابن عباس - رضي الله عنهما - قال : "جَاءَ أعْرَابِيٌّ إلَى النَّبيِّ - صلى الله عليه وسلم فَقالَ : إنِّي رَأَيْتُ الهِلاَلَ ، فَقالَ : أتَشْهَدُ أنْ لاَ إلهَ إلاَّ الله؟ ، قال : نَعَمْ ، قالَ : أتَشْهَدُ أنَّ مُحمَّداً رَسُولُ الله؟ ، قال : نَعَمْ ، قالَ : يَا بِلاَلُ أذِّنْ في النَّاسِ فَلْيَصُوموا غَداً"] أخرجه أبو داود في سننه في كتاب الصيام / باب في شهادة الواحد على رؤية هلال رمضان (2341) ، والترمذي في سننه في كتاب الصوم / بابُ ما جَاء في الصَّوْمِ بالشَّهَادَة (685) ، والنسائي في سننه في كتاب الصيام / باب قبول شهادة الرجل الواحد على هلال شهر رمضان وذكر الاختلاف فيه على سفيان في حديث سماك (2113) ، وابن ماجه في سننه في كتاب الصيام / باب ما جاء في الشهادة على رؤية الهلال (1702) ، قال عنه الألباني : ضعيف [ضعيف سنن أبي داود للإمام الألباني (صـ 182) رقم الحديث (2340)]
Daga Ibn Abbas(r.a) yace” Wani Balaraben Kauye yazo wajen Manzon Allaah Sallallahu Alaihi Wasallam yace: 
“NI NAGA JINJIRIN WATA”.
Sai Manzon Allaah(s.a.w) yace dashi:
”SHIN KA SHAIDA BABU WANDA YA CANCANTA A BAUTAWA SAI ALLAAH?. Sai yace’NAAM’.
Sai Manzon Allaah(s.a.w) ya kuma cewa dashi:”SHIN KA SHAIDA MUHAMMAD MANZON ALLAH NE?” Sai yace ‘NAAM’.
Sai Manzon Allaah(s.a.w) yace:
”YA BILAL(r.a)! KA SANAR DA MUTANE SU TASHI DA AZUMI GOBE”.
Koda yake shi Hadeethi na biyu Sheikh Albani(r) ya Raunanashi,amma yana nuni da alamar Hadeethin farko.

Wan nan sai yake nuna cewa matukar Mutum Musulmi ne,ana iya karbar Shaidarsa a wajen ganin Wata, kodashi kadai yace ya gani,bisa yanda shugaba ya gamsu da dalilansa,ko kuma  misalan daya kawo masa,ko kuma gamsuwa da amsoshin Tambayoyin da yayi masa.

Akan haka ne Malaman Shafi’iyyah dana hanbaliyyah suka tafi.
S
ai dai su Malaman Hanabilah basu sanya Sharadin mutum yazama ‘Da ko Namiji ba’. 
A inda Shafi’iyyah sukace Dolene ya zama ‘'Namiji amma ba za’a karbi Shaidar Mace ita kadai ba'’.

Su kuwa Malaman Malikiyyah sukace: 
“Ba za’a karbi shaidar mutum guda ba,sai daisu zama mutane guda biyu,kuma Adalai’.
Malaman Hanafiyyah kuwa,sunyi Tafsilin Maganar ne,sukace:

IDAN SAMA TANA DA GIRGIJE TAYI DUHU,KO KUMA WANI ABU DAYA HANA GANIN WATA,TO AKAN WATAN RAMADHAN AN KARBAR SHAIDA MUTUM GUDA,KUMA BABU SHARADIN YA ZAMA ‘DA KO NAMIJI.
AMMA IDAN SAMA GARAU TAKE BABU WANI ABU DA ZAI HANA AGA WATA,TO DOLE SAI IDAN AN SAMU SHAIDA DAGA JAMA’A MASU YAWA,KUMA JAMA’AR MASU YAWA YANA GA WAJEN SHUGABA,IDAN YACE YAWANSU YA ISA HAKA DIN”.
Malam ya kawo wa’yan nan bayanai filla kamar haka:
وهذا هو قول الحنابلة .[الإنصاف] للمرداوي (3\194)[ والشافعية .[المجموع] للنووي (6\184)[.
وعلى مذهب الحنابلة لا يُشترط كون الشاهد هنا ذكراً ولا حراً ، ولا أن تكون بلفظ الشهادة.
وأما مذهب الشافعية فلا يقبلون هنا شهادة المرأة ولا العبد. [المجموع] للنووي (6\184)[
وأما مذهب المالكية فلا يقبلون هنا إلا أن يشهد عدلان بذلك. [المدونة الكبرى] للإمام مالك (1\193)]
وأما مذهب الحنفية ففيه تفصيل : إن كان بالسماء علة - أي غيم أو قتر أو نحوهما - فشهادة الواحد على هلال رمضان مقبولة ، وفي هذه الحالة لا يشترطون كونه ذكراً ولا حراً ، وإن لم يكن بالسماء علة فلا تقبل إلا شهادة جمع كثير يقع العلم بخبرهم ، وتقدير ذلك الجمع مفوّض إلى الإمام [الفتاوى الهندية] للهمام مولانا الشيخ نظام[ 1\217- 218).

Wa’yan nan duk domin gujewa sabanin rashin ilimin al’amarin akan harkar ganin wata.

Amma abin mamaki sai kaga mutane basu damu da Nassi ko kuma fahimtar Magabataba,sai kawai suyiwa shugabanni tawaye akan ganin wata.
Allah yasa mu dace!!

نسأل الله تعالى أن يجعلنا وإياكم من عتقاء النار وأن يرحمنا ويغفر لنا وان يعيد علينا رمضان مرات عديدة وكرات مديدة.
وآخر دعوانا أن الحمد لله رب العالمين
AZUMI A MAHANGAR SHARIA(4)
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيم ، والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وأصحابه ومن ولاه

Azumi yana tabbata ya zama wajibi akan Musulmai da dayan abubuwa guda biyu.

1- Ganin Jinjirin wata na Ramadhadan.

2-Cikar watan Sha’aban kwana talatin(30) dai dai.

Wan nan shine Sharia ta tsayar bisa hujjoji daga  Allaah swt da  kuma Sunnar Manzon Allaah(s.a.w).

Allaah yace
فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ
“DUK WANDA YA HALARCESHI(watan Ramadhan) TO YA AZUMCESHI”

Ma’ana wanda akaga wata kuma yana raye to yayi Azumin wantan Ramadhana, bashi nufin sai kowa yaga Watan da kansa.

Manzon Allaah(s.a.w) yace:
«إِذَا رأيتُمُ الهلالَ فصوموا»
“IDAN KUKAGA JINJIRIN WATA,TO KU AZUMCESHI”

Hanyoyin da ake tabbatar da ganin wata daga Bakin Manzon Allaah(s.a.w).

A-Idan anga jinjirin wata domin Manzon Allaah(s.a.w) yace:
فقالَ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِذَا رَأيتُمُ الهلالَ فصُوموا وإِذَا رَأَيْتُمُوه فأفْطِروا»، متفق عليه
“IDAN KUNGA JINJIRIN WATA TO KU AZUMCESHI,HAKA KUMA IDAN KUNGANSHI TO KU CI(lokacin Sallah)”.

Haka kuma yazo daga gareshi dai yace:
قال صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إن شَهِدَ شاهدان مُسْلمانِ فصومُوا وأفْطُروا»، رواه أحمد  .[إسناده لا بأس به على اختلاف فيه وله شاهد عند أبي داود والدارقطني وقال: هذا إسناده متصل صحيح].
“IDAN MUSULMAI GUDA BIYU SUKA SHAIDA SUNGA WATA,TO KUYI AZUMI,KUMA KUCI(idan watan Shawwal ne)”.
[Sai dai wan nan ruwayar bata da laifi a bisa sabani, kuma a wajen Abu Daud da Daruqud'niy akwai Shahid,har ya kara da cewa isnadinsa ya sadu kuma Saheehi ne].

B-Cikar watan Sha’aban kwana 30 koda ba’aga watan ba indai yakai kwana talatin to Azumi ya kama,saboda fadin Manzon Allaah(s.a.w):
«صُوموا لِرؤيتِهِ وأفْطروا لرؤيته فإن غُمِّي عليكُمْ الشهر فعدوا ثلاثين»، رواهُ مسلم.
‘KUYI AZUMI SABODA GANIN WATA,KUMA KUCI SABODA GANINSA,AMMA IDAN AKA BOYE MUKU WATAN,TO KU KIRGA KWANA TALATIN”.

Wan nan yana nuna cewa wata yakan zamo kwana ishirin da tara(29) mafi yawa,ko kuma Talatin(30) idan ba’a ganshi ba.

Sau da yawa Watanni a jere sukan yi kwanaki 29,kamar wata 2,3 ko 4.
Haka kuma sukanyi kwanaki 30 a jere shima kamar yanda muka fada a sama.
Wata hikima ta Manzon Allaah(s.a.w), sai yace”Idan aka boye muku shi, to sai ku kidaya masa 30,ashe asalinsa 29 ne,saifa idan ba’a ganshi ba,kodai anyi girgije ko kuma dai wani dalili,to sai a kirga 30.

Domin fito da hukuncin fili, sai Aishah(r.a) tace:
«كانَ النبيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَتحفَّظُ من شعبانَ ما لا يَتَحَفَّظ من غيرهِ ثم يصوم لرؤيةِ رمضان فإنْ غُمَّ عليه عَدَّ ثلاثين يوماً ثم صام»، وأخرجه أيضاً أبو دَاود والدَّارقطنيُّ وصحَّحهُ.
“MANZON ALLAAH(S.A.W) YA ZAMA YANA KIYAYE WATAN SHA’ABAN FIYE DA KO WANE WATA,SAN NAN KUMA SAI YAYI AZUMI IDAN ANGA RAMADHANA. 
AMMA IDAN AKA BOYE MISHI WATAN,SAI YA KIRGA KWANA TALATIN,SAN NAN YA DAUKI AZUMI”.

Wan nan yana kara fito da Mas’alar ganin wata fili,cewa kodai kwana 29 ne da ganin wata,ko kuma 30 koda watan ya buya.
Hadeethin da Manzon Allaah(s.a.w) yayiwa Matansa Yaji tsawon Wata guda ya kuma fito da batun fili.

Domin bayan kwana 29 daya shigo gida,sai Matarsa dayafi so tace,bakace wata guda ba ne?  Gashi kuma yau kwana 29.
Sai yace ai Wata kwana 29 ne.

Ruwayar Abdullahi ibn Umar(r.a) ta kara fito da batun a sarari kamar haka:
عن نافع عن ابن عمر - رضي الله عنهما - قال : قال رسول الله - صلى الله عليه وسلم - : "إِنَّمَا الشَّهْرُ تِسْعٌ وَعِشْرُونَ فَلاَ تَصُومُوا حَتَّى تَرَوْهُ، وَلاَ تُفْطِرُوا حَتَّى تَرَوْهُ، فَإِنْ غُمَّ عَلَيْكُمْ فَاقْدِرُوا لَهُ"] أخرجه أبو داود في سننه في كتاب الصيام / باب الشهر يكون تسعاً وعشرين (2321) ، وأحمد في مسنده (4483) ، قال الألباني عن حديث ابن عمر - رضي الله عنهما - : صحيح دون قوله (فكان ابن عمر) [صحيح سنن أبي داود للإمام الألباني (2\49) رقم الحديث (2320)]
“Manzon Allaah(s.a.w) yace:
‘'WATA KWANA ASHIRIN DA TARANE(29), KADA KUYI AZUMI HAR SAI KUN GANSHI,KADA KUMA KUCI HAR SAI KUN GANSHI.
AMMA IDAN YA BUYA GAREKU, TO KU KIRGA MISHI”.

Haka ya kuma zuwa cikin fadin Manzon Allaah(s.a.w) yace:
“عن النبيِّ - صلى الله عليه وسلم - أنهُ قال: "إنّا أُمَّةٌ أُمِّيةٌ لا نَكتُبُ ولا نَحسُبُ ، الشهرُ هكذا وهكذا. يَعني مرَّةً تسعةً وعشرينَ ومرَّةً ثلاثين".
“LALLAI MU MUTANE NE UMMIYYAI, BAMA RUBUTU KUMA BAMA(rubuta) LISSAFI, WATA DAI HAKA NE DA KUMA HAKA(na farko ya lankwashe yatsansa daya,bayan ya kirga yatsunsa su uku)”.
Yana nufin wani lokaci 29,wani kuma lokaci 30.

Idan Musulmi yasan wa’yan nan maganganu daga bakin fiyayyen Halitta,ina batun Gardama idan wata yayi kwana 29 ko kuma 30?
Allaah ya shiryar damu!!!

Maganganun Malaman Mazhabobi akan ganin Wata,da kuma suwaye idan sunga wata ake yarda dasu.
Su waye ya kamata su sanar da anga wata???.

Idan anga Wata amma Shugaba bai yarda da masu ganin ba menene hukuncin ganin Watan nasu,kuma me yakamata suyi???

نسأل الله تعالى أن يجعلنا وإياكم من عتقاء النار وأن يرحمنا ويغفر لنا وان يعيد علينا رمضان مرات عديدة وكرات مديدة.
وآخر دعوانا أن الحمد لله رب العالمين
AZUMI A MAHANGAR SHARIA(3)
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيم ، والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وأصحابه ومن ولاه

Menene matsayin Azumin Ramdhana akan Musulmai, kuma akan suwa ya zama Wajibi?

Azumin watan Ramadhana  dayan Rukunine a cikin Rukunnan Musulunci kuma   Wajibi ne akan Musulmi , Baligi, mai Hankali kuma mai ikon yin Azumin.
Wajibine  Azumin Ramadhana a cikin Alqur’aani da Sunnah da kuma ijima’in Malaman musulunci.

A Alqur’aani Allaah yace”
قَالَ اللهُ تعالى:{يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ أَيَّاماً مَعْدُودَاتٍ فَمَنْ كَانَ مِنْكُمْ مَرِيضاً أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ فَمَنْ تَطَوَّعَ خَيْراً فَهُوَ خَيْرٌ لَهُ وَأَنْ تَصُومُوا خَيْرٌ لَكُمْ إِنْ كُنْتُمْ تَعْلَمُونَ شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ هُدىً لِلنَّاسِ وَبَيِّنَاتٍ مِنَ الْهُدَى وَالْفُرْقَانِ فَمَنْ شَهِدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ وَمَنْ كَانَ مَرِيضاً أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ يُرِيدُ اللهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْرَ وَلِتُكْمِلُوا الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللهَ عَلَى مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ} [البقرة: 183-185]
“YAKU WA’YANDA KUKA BADA GASKIYA, AN WAJABTA MUKU AZUMI,KAMAR YANDA AKA WAJABTAWA WA’YANDA SUKAZO KAFINKU, DOMIN KUYI TAQWA. KWANAKI KIRGAGGU,AMMA WANDA YAZAMA BASHI DA LAFIYA DAKA CIKUNKU KO KUMA YA ZAM MATAFIYI TO YA KIDAYA WASU RANEKUN DABAM, HAKA WANDA  BAZAI IYA YIBA TO YA BADA FANSA TA CIYAR DA MISKINAI, WANDA KUMA YAYI KARI AKAN FANSA TO SHINE MAFI ALKHAIRI A GARESHI,AMMA FA YIN AZUMIN SHINE YAFI ALKHAIRI.
WATAN RAMADHAN A CIKIN SANE AKA SAUKAR DA ALQUR’AANI WANDA SHIRIYA NE GA MUTANE,KUMA BAYANI AKAN SHIRIYA KUMA MAI RARRABEWA NE{tsakanin karya da gaskiya].
WANDA YA ZAMA YANA HALARCE WATAN YAZO A CIKUNKU TO YAYI AZUMIN,AMMA WANDA YAKE BASHI DA LAFIYA KO KUMA YA ZAM MATAFIYI TO YA KIDAYA WASU KWANAKIN[na daban]. 
ALLAAH YANA NUFIN SAUKI NE A GAREKU,BAYA NUFIN TSANANI A GAREKU,DON HAKA KU CIKA KWANAKIN KU, KUMA GIRMAMA ALLAAH AKAN SHIRIYAR DA YAYI MUKU, DOMIN KU ZAMA MASU GODIYA”.

Wan ayar itace take nuna Wajbcin Azumi akan Musulmai,kuma tana dauke da wasu  hukunce hukunce daya rataya da mai Azumin.

Haka kuma tana cikin Ayar data raba Azumi zuwa Marhala guda biyu(2).

A farko ana bada zabi ko ayi shi[Azumin] ko a bari,san nan kuma ayar baya tazo da wajabcin yinsa.

Yazo a cikin Bukhari da muslim daga Salamah Dan  Ak’wa’(r.a)  yace:
ففي الصحيحين عن سَلَمة بن الأكوع رضي الله عنه قال لما نَزَلَتْ: {وَعَلَى الَّذِينَ يُطِيقُونَهُ فِدْيَةٌ طَعَامُ مِسْكِينٍ } كان مَنْ أرَاد أن يُفْطِر ويفْتديَ «يعني فَعَل» حتى نَزَلَتْ الآيةُ التي بَعْدَها فَنَسخَتْها يَعْني بها قولهُ تَعالى: {فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ وَمَن كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِّنْ أَيَّامٍ أُخَرَ} فَأوْجَب الله الصيامَ عَيْناً بِدُونَ تَخْيير.

“YAYIN DA AKA SAUKAR DA: "AMMA WA’YANDA ZASU SAMI WAHALA WAJEN YIN AZUMIN,TO SU BADA FANSAR CIYAR DA MISKINI’. 
SAI WANDA YAGA  DAMA YACI KUMA YA CIYAR .
HAR SAI DA AKA SAUKAR DA AYAR BAYANTA WACCE TACE: "DUK WANDA YA ZAMO WATA YA SHIGO YANA NAN, TO YA AZUMCESHI,KUMA WANDA YA ZAMA BASHI DA LAFIYA KO KUMA MATAFIYI,TO YAYI KIRGAR KWANAKIN DA YASHA. SAI ALLAAH YA WAJABTA AZUMI BABU ZABI”.

Daga Sunnar Manzon Allaah(s.a.w) kuwa:
Manzon Allaah(s.a.w) yace:
وقال النبي صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «بُنِي الإِسلامُ على خَمْسٍ: شهادةِ أنْ لا إِله إِلاَّ الله وأنَّ محمداً رسولُ الله، وإقام الصلاةِ، وإيتاءِ الزكاةِ، وحَجِّ الْبَيْتِ، وَصومِ رمضانَ»، متفق عليه.

“AN GINA MUSULUNCI AKAN ABUBUWA GUDA BIYAR:
1- Shaidawa babu wanda za’a bautawa bisa cancnta Sai Allaah, kuma Muhammad(s.a.w) Manzonsa ne.

2-Tsaida Sallah.

3- Bada Zakkah

4- Zuwa aikin Hajji.

5-Azumtar watan Ramadhana.

A wata ruwaya ta muslim kuwa sai ya fara kawo Azumtar watan Ramadhana kafin aikin hajji.

Saboda wa’yan nan dalilai dukkan musulmai kuma suka hadu akan cewa Azumin watan Ramadhana Wajibi ne.

Azumin Ramadhana yana zama wajibi ga Musulmi da shigowar Watan,wato ganin Jinjirin Watan,ko kuma cikar Watan Sha’abana kwana Talatin(30).

Da zarar daya daga cikin wa’yan nan ya faru,to Azumi ya zama dole akan al’ummar musulmai.
Alqur’aani yace”
فَمَن شَهِدَ مِنكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ
“DUK WANDA YA HALARCESHI(watan Ramadhan) TO YA AZUMCESHI”.

San nan Manzon Allaah(s.a.w) yace:
«إِذَا رأيتُمُ الهلالَ فصوموا»
“IDAN KUKAGA JINJIRIN WATA,TO KU AZUMCESHI”.

Wan nan kuma baya nufin kowa sai yaga Watan da idonsa kiri kiri bane,matukar wani ya gani,kuma hukuma ta bada Sanarwa to Wajibi ne akan Musulmai su dauki Azumin.
Zamuci gaba inshaAllaah.

نسأل الله تعالى أن يجعلنا وإياكم من عتقاء النار وأن يرحمنا ويغفر لنا وان يعيد علينا رمضان مرات عديدة وكرات مديدة.
وآخر دعوانا أن الحمد لله رب العالمين
AZUMI A MAHANGAR SHARIA(2)

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيم ، والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وأصحابه ومن ولاه

Yana daga cikin falalolin Azumin watan Ramadhana,Manzon Allaah(s.a.w)yace”
قال رسول الله (صلى الله عليه وسلم ) :( أتاكم رمضان شهر مبارك فرض الله عز وجل عليكم صيامه تفتح فيه أبواب السماء وتغلق فيه أبواب الجحيم وتغل فيه مردة الشياطين لله فيه ليلة خير من ألف شهر من حرم خيرها فقد حرم ) (صحيح رواه أحمد 9/225 ( الفتح الرباني ) والنسائي 4/129 وصححه الألباني في الترغيب 1/490).
“WATAN RAMADHANA YAZO MUKU,WATA MAI ALBARKA,ALLAAH MADAUKAKIN SARKI YA WAJABTA MUKU AZUMTARSA, ANA BUDE KOFOFIN SAMMAI ACIKINSA,ANA KUMA KULLE KOFOFIN JAHANNAMA A CIKINSA,ANA KUMA DAURE KANGARARRUN  SHAIDANU A CIKINSA,ALLAAH KUWA CIKINSA AKWAI DARE WANDA YAFI DAREN WATA DUBU,WANDA DUK AKA HARAMTA MASA ALKHAIRIN WATAN,TO TABBAS AN HARAMTA MASA(alkhairi mai yawa)”.

Haka kuma yazo a cikin Bukhari da Muslim daga Manzon Allaah(s.a.w) cikin abinda ya rawaito daga Mahaliccinsa  yace”
ففي الصحيحين ( البخاري 4/103 ومسلم 2/802 ) عن أبي هريرة رضي الله عنه قال : قال رسول الله (صلى الله عليه وسلم) : قال الله تعالي " كل عمل ابن آدم له إلا الصوم فإنه لي وأنا أجزي به, والصيام جنة فإذا كان يوم صوم أحدكم فلا يرفث ولا يصخب فإن سابه أحد أو قاتله فليقل إني صائم والذي نفس محمد بيده لخلوف فم الصائم أطيب عند الله من ريح المسك وللصائم فرحتان يفرحهما إذا أفطر فرح بفطره وإذا لقي ربه فرح بصومه".
“ ALLAAH SWT YACE ‘KOWANE AIKI NA DAN ADAM NASA NE,SAI AZUMI KAWAI NINE ZAN SAKA MASA DANSHI, AZUMI GARKUWA NE, IDAN DAYANKU YANA AZUMI,KADA YAYI KWARKWASA,KADA KUMA YAYI HAYANIYA,IDAN WANI YA ZAGESHI, KO KUMA YAYI RIKICI DASHI,YACE MASA NI INA YIN AZUMI. 
NA RANTSE DA WANDA RAN MUHAMMAD (s.a.w) YAKE HANNUNSA,WARIN BAKIN MAI AZUMI,SHI YAFI KAMSHI DAGA ALMISKI A WAJEN ALLAH. 
AKWAI FARIN CIKI GUDA BIYU GA MAI YIN AZUMI,FARIN CIKI LOKACIN BUDA BAKI SAI YAYI FARIN CIKIN ABINDA ZAICI,DA KUMA FARIN CIKI LOKACIN DA ZAI HADU DA MAHALICCINSA,SAI YAYI FARIN CIKI DA AZUMIN DA YAYI”.

Tabbas mai Azumi yana yin matukar farin ciki lokacinda zai buda bakinsa,domin bayan yasha yunwa da kishirwa,kuma gashi Allaah ya kawoshi lokacinda zaici abinci, san nan kuma zaiyi farin cikin haduwa da Allaah yana mai karbar ladan Azuminsa.
Wani abu mai kuma kara burgewa da sanya nishadi shine, saboda dadewa mutum baici komai ba, hanjinsa zai ringa fitar da wani sinadari mai wari,amma kuma shi wan nan warin,maimakon ya zama mai bata masa rai,sai Allaah ya tabbatar masa cewar yafi jin kamshinsa fiye da turaren Almiski.

Kuma dai yana daga cikin Falalar Azumi,kankare zunuban shekara mutukar Mutum ya guji manyan zunubai.
Manzon Allaah(s.a.w) yace:
وفي صحيح مسلم ( 233 ) عن أبي هريرة رضي الله عنه أيضاً أن النبي (صلى الله عليه وسلم) قال : " الصلوات الخمس والجمعة إلي الجمعة ورمضان إلي رمضان مكفرات ما بينهن إذا اجتنبت الكبائر".
“SALLOLI GUDA BIYAR A RANA, DA KUMA SALLAR JUMA’A ZUWA WATA JUMA’AR,DA KUMA RAMADHANA ZUWA RAMADHANA,MASU KANKARE ZUNUBAN DAKE TSAKANINSU NE,MUTUKAR MUTUM YA GUJI MANYAN ZUNUBAI”.

Manzon Allah(s.a.w) yace:
قال رسول الله (صلى الله عليه وسلم) " من قام ليلة القدر إيماناً واحتساباً غُفر له ما تقدم من ذنبه ومن صام رمضان إيمانا واحتسابا غفر له ما تقدم من ذنبه "
( أخرجه البخاري 3/59 ومسلم 1/524 رقم 175 ).
“WANDA DUK YA TSAYAWA DAREN LAILAILATUL-QADR YANA MAI IMANI, YANA KUMA MAI NEMAN LADA AN GAFARTA MASA ZUNUBANSA DA SUKA GABATA,HAKA DUK WANDA YA AZUMCI RAMADHANA, YANA MAI IMANI KUMA YANA MAI NEMAN LADA,SHIMA AN GAFARTA MASA ZUNUBANSA DA SUKA GABATA”.

Malamai sukace matukar mutum yayi Azumin watan Ramadhana, yana mai imani da Allaah da kuma imani cewa wajibine akansa yayi Azumin,kuma yana mai neman ladan Azumin a wajen Allaah shi kadai,babu riya kuma babu neman jiyarwa,to lallai Allaah ya gafarta masa zunubansa wa’yanda suka gabata.
Akwai Falala mai yawan gaske ga ita wan nan ibadah ta Azumi.
Zamuci gaba inshaAllaah.

San nan zamu kawo sharudda da kuma wa’yanda Azumi ya wajaba akansu gwargwadon iko a gaba da yardar Allaah.
نسأل الله تعالى ن يجعلنا وإياكم من عتقاء النار وأن يرحمنا ويغفر لنا وان يعيد علينا رمضان مرات عديدة وكرات مديدة.
وآخر دعوانا أن الحمد لله رب العالمين