Sunday, 30 June 2013

  • AZUMI A MAHANGAR SHARIA(1)

    بِسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
    إن الحمدَ لله نحمدُه ونستعينهُ، ونستغفره ونتوب إليه، ونعوذ بالله من شرورِ أنفسِنا ومن سيئاتِ أعمالِنا. من يهدِه اللهُ فلا مضلَ له، ومن يضلِلْ فلا هاديَ له، وأشهدُ أن لا إِلهَ إِلاَّ اللهُ وحدَه لا شريكَ له، وأشهدُ أن محمداً عبدُه ورسولُه صلَّى الله عليه وعلى آلِه وأصحابِه ومن تبعهم بإِحسانٍ إلى يومِ الدين وسلَّم تسليماً.

    Zamu fara Magana akan Azumin watan Ramadhana,saboda kasancewarsa yana tafe,muna fata Allaah ya tsarkake nniyarmu ya kuma sanyashi cikin mizaninmu na Alkhairi.

    Zamuyi kokarin kawo bayanai akan Azumi gwargwadon fahimta akan koyarwar Manzon Allaah(s.a.w), da ayyukan da Manzon Allaah(s.a.w) yakeyi cikin watan Ramadhan.
    San nan mu kawo yanda ya keyin Tsayuwar Ramadhana,da siffofin tsayuwar, da yanda aka samu ruwayoyin Hadeethai bisa koyarwar Annabi(s.a.w) da kuma Sahabbansa da Magaabata na gari.
    Allaah muke roko ya bamu ikon yin dai dai,ya kuma azurtamu da aiki da dai dai din.

    Ina kira ga ‘Yan uwa Malamaina da kuma Dalibai irina da idan anga gyara cikin abinda zamu fada, ayi sauri a gyara mana,saboda kada a bari wasu su dauki kuskure suyi aiki dashi.
    Dukkan abinda yake dai dai daga Allaah da Manzonsa(s.a.w) ne,kuma idan akaga kuskure to daga nine da kuma Shaidan!!
    Watan Ramadhana wani wata ne mai muhimmanci a gurin musulmai,kuma watane wanda yake tare da Alkhairai masu din bin yawa.

    Bayin Allaah na gargaru suna yin tsawon wat shida suna tattali da kuma rokon Allah yakaisu shi wan nan wata,kuma sunayin wani wata shidan suna rokon Allaah ya karba musu aiyukansu da sukayi cikin Ramadhana.
    Wani Malami a cikin littafinsa mai suna:
    “مجالس رمضانية”
    Ya kawo wan nan baynin kamar haka:
    قال معلى بن الفضل : كانوا (السلف) يدعون الله تعالى ستة أشهر أن يُبلغهم رمضان, ثم يدعونه ستة أشهر أن يتقبل منهم. وقال يحيى بن أبي كثير : كان من دعائهم : اللهم سلمني إلى رمضان, وسلم لي رمضان, وتسلمه مني متقبلاً
    MU’ALLA’ BN FADHL YACE: SALAF SUN KASANCE SUNA ROKON ALLAAH MADAUKAKIN SARKI TSAWON WATA SHIDA YA KAISU ZUWA RAMADHANA,SAN NAN KUMA SUNA ROKONSAA TSAWON WATA SHIDA YA KARBA MUSU(ayyukansu cikinsa).

    Malam Yahya bn Abi Katheer yace: YANA DAGA CIKIN ADDU’ARSU SUNA CEWA”YA ALLAAH KA AMINCE MANA ZUWA RAMADHANA, KA AMINCEWA RAMADHANA ZUWAMMANA, KA KUMA AMINCE MAN SHI DA KARBAR AYYUKANMU”.
    Watan Ramdhana wata ne daya kebanta da Falaloli masu dinbin yawa,kadan daga cikinsu shine:
    1-DAURE SHAIDANU, BUDE KOFOFIN ALJANNAH DA KUMA KULLE KOFOFIN WUTA:
    ففي الصحيحين عن أبي هريرة - رضي الله عنه - ، أن النبي - صلي الله عليه وسلم - قال :" إذا جاء رمضان فتحت أبواب الجنة وغلقت أبواب النار وصفدت الشياطين "
    Yazo cikin Bukhari da Muslim,daga Abu Hurairah(r.a), Manzon Allah(s.a.w) yace:”IDAN RAMADHANA YAZO,ANA BUDE KOFOFIN ALJANNAH,SAN NAN KUMA ANA KULLE KOFOFIN WUTA,ANA KUMA DAUREN SHAIDANU(na Aljannu masu sanya sharri).
    Idan muka fahimci hadeethin, ya kawo abubuwa guda uku da suke faruwa cikin Ramadhana.

    a- Bude kofofin Aljannah cikin wata domin bawa mumunai damar shigarta.

    b- Kulle kofofin wuta,saboda kare Mumunai dag shigarta cikin shi wan nan wata mai albarka.

    c- Daure Shaidanu domin bawa mumunai damar yin aiki ba tareda sun kawo musu cikas ba.
    Don hakane ma Manzon Allaah(s.a.w) yace:”
     ( إذا كان أول ليلة من شهر رمضان صفدت الشياطين ومردة الجن وغُلقت أبواب النيران فلم يفتح منها باب وفتحت أبواب الجنة فلم يغلق منها باب وينادي مناد يا باغي الخير أقبل ويا باغي الشر أقصر ولله عتقاء من النار وذلك كل ليلة ) " ]رواه الترمذي 3/359 وابن ماجة 1642 وهو حسن".[
    “IDAN FARKON DAREN WATAN RAMADHANA YA SHIGO,ANA DAURE SHAIDANU DA KUMA KANGARARRUN ALJANU,SN NAN KUMA A KULLE KOFOFIN WUTA BAZA’A BUDESU BA.
    SAN NAN KUMA A BUDE KOFOFIN ALJANNAH, BAZA’A RUFESUBA,SAI MAI KIRA YA RINGA KIRA YANA CEWA,YA MA’ABOCIN ALKHAIRI GABATO,YA KAI MA’ABOCIN SHARRI TAKAITA,A KOWANE DRE AKWAI WA’YANDA ALLAH YAKE ‘YANTAWA DAGA BARIN SHIGA WUTA”.
    An tambyi Manzon Allah cewa,shin wan nan a ranar Lailatul-Qadri ne kawai,sai yace a’a akowane dare cikin Ramadhana.
    Yana daga cikin wan nan dalilan nema Manzon Allaah(s.a.w) yayi wata addu’a ga mutane guda biyu yace”
    رغم أنف رجل دخل عليه رمضان ثم انسلخ قبل أن يُغفر له, ورغم أنف رجل أدرك عنده أبواه الكبر فلم يدخلاه الجنة" (رواه الترمذي وصححه الألباني في صحيح الجامع 3510).
    “AN TURBUDA HANCIN WANDA RAMADHANA YA SHIGA YANA NAN,SAN NAN KUMA YA FITA BA’AYI MASA GAFARA BA.
    AN TURBUDA HANCIN MUTUMIN DA GIRMA YA RISKI IYAYENSA YANA TARE DASU,AMMA BAIYI ABINDA ZA’A SHIGAR DASHI ALJANNAH BA SABODA KYAUTATA MUSU”.
    Hakika Watan Ramadhana yana tare da darajoji da kuma falaloli masu yawa,kuma hanyace ta kai mutum Aljannah idan ya ganimanceshi.
    Zamuci gaba inshaAllaah.
    نسأل الله تعالى ن يجعلنا وإياكم من عتقاء النار وأن يرحمنا ويغفر لنا وان يعيد علينا رمضان مرات عديدة وكرات مديدة.
    وآخر دعوانا أن الحمد لله رب العالمين